Hausa - Gumi : Aka ce mata "Ki shiga a gidan sarauta" To a lõkacin da ta gan shi ta yi zatona wai gurbi ne kuma ta kuranye daga ƙwaurinta Ya ce "Lalle ne shi gidan sarauta ne mai santsi daga madũbai" Ta ce "Yã Ubangijĩna Bã a rõƙon Allah sai da sunãyensa mãsu kyau tis'in da taran nan sai dai a dunƙule kamar a ce "Inã rõƙon Allah da sunãyenSa da na sani da waɗanda ban sani ba" Lalle nĩ na zãlunci kaina kuma nã sallama al'amari tãre da Sulaiman ga Allah Ubangijin halittu"